An samu rasuwa da jikkatar mutane a rugujewar wani gini a Jigawa, shugabanni sun ce a kula

39

Wani mutum ya rasa ransa yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon rugujewar wani gini a ƙauyen Kabak, cikin Ƙaramar Hukumar Kirikasamma, Jihar Jigawa.

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da Times Hausa ta samu.

Wakilinmu ya tattaro daga Musa Muhammad cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a yankin Kirikasamma da kewaye, inda ya bayyana cewa, “An samu mutum guda da ya rasu yayin da wasu mutane bakwai suka samu munanan raunuka a ƙauyen Kabak na Kirikasamma. Lamarin ya faru ne da tsakar dare a ranar Juma’a, inda aka kwantar da marasa lafiya guda biyar a asibiti, yayin da daga baya aka sallami biyu sauran ukun na ci gaba da karɓar magani,” in ji shi.

Jami’in yaɗa labaran ya ƙara bayyana cewa, Shugaban Ƙaramar Hukumar, Muhammad Maji, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da bayar da gudunmawar kuɗi domin sauƙaƙa musu rayuwa.

Sanarwar ta ƙara bayyana cewa, an bayar da ₦500,000 domin biyan kuɗin jinyar marasa lafiyar da suka ji rauni, tare da ₦100,000 a matsayin taimakon gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasu.

Sanarwar ta buƙaci al’umma da su kula, tare da kai rahoton ruɓaɓbun gine-gine don gudun ƙara faruwar hakan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.