ADC ta gargaɗi ƴan sanda da gwamnati, “Ku daina tsoratar da shugabanninmu, ku fuskanci ƴan ta’adda

12

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi gargaɗi ga Gwamnatin Tarayya da Hukumar Ƴan Sanda ta Najeriya kan abin da ta kira mummunan tsoratar da shugabannin jam’iyyun adawa, tana mai kiran jami’an tsaro su mayar da hankali wajen yaƙi da ta’addanci da masu aikata manyan laifuka da ke addabar ƙasar.

Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da Mallam Bolaji Abdullahi, Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa ya sa wa hannu a kai, cewa ADC ta la’anci takardar gayyatar da ƴan sanda suka aika wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, da kuma harin da aka kai wa tawagar tsohon Babban Lauyan Ƙasa, Abubakar Malami (SAN), a Birnin Kebbi, inda aka jikkata wasu mambobin jam’iyyar.

Harin, wanda aka kai a bainar jama’a, ya auku ne a kusa da ofishin ƴan sanda, amma ba a cafke kowa kan laifin ba har kawo yanzu.

“A wannan lokaci da ƴan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata miyagun laifuka ke yawo cikin ƴanci a yankunan Arewa, ƴan sandan Najeriya sun fi mayar da hankali wajen murƙushe shugabannin jam’iyyun adawa maimakon kare rayukan ƴan ƙasa,” in ji sanarwar.

“Maimakon su kama waɗanda suka kai hari kan tarurrukan jam’iyyarmu, yanzu ana tursasawa waɗanda aka zalunta da takardun gayyata. Wannan ba wai mutum ɗaya kawai ya shafa ba – babban cin fuska ne ga demokaraɗiyya a Najeriya.”

Jam’iyyar ta ce a Kaduna, wasu ƴan daba ɗauke da duwatsu da takubba sun tarwatsa taron jam’iyyar da ake yi cikin salama, haka kuma a Kebbi, an kai wa Malami hari a bainar jama’a, duk da haka ba a kama ko da mutum ɗaya daga cikin masu laifin ba.

“Duk da abin ya yi muni, amma har yanzu ba a damƙe waɗanda suka aikata laifin ba,” sanarwar ta ƙara da cewa, tana gargaɗin cewa amincewar jama’a ga hukumar ƴan sanda na iya rushewa idan aka ci gaba da ganin ta a matsayin “kayan aikin danniyar siyasa maimakon cibiyar tsaro ta ƙasa.”

ADC ta yi kira ga ƴan Najeriya da su lura da wannan al’amari mai hatsari tare da kiran gwamnatin tarayya ta umurci jami’an tsaro su koma kan aikinsu na kare rayuka, dukiyoyi, da tabbatar da adalci a cikin tsarin demokaraɗiyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.