Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tana kula da matakin da gwamnati ke ɗauka na naɗa Farfesa Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), amma tana fatan zai tabbatar da sahihin shugabanci mai gaskiya da inganci.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce sabon shugaban INEC dole ne ya nuna kishin ƙasa fiye da kowace manufa ta gwamnati.
“Dole ne ya fahimci cewa amincewar da yake da ita daga ƴan Najeriya take, ba daga gwamnati kawai ba,” in ji shi.
Abdullahi ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta ba shi damar nuna ƙwarewarsa, duba da tarihin aikinsa da ya gabata, amma yanzu dama ce gare shi ya rubuta sunansa cikin tarihin nagarta ko kuma ya ɓata shi da aikata akasin haka.
“Ya kamata ya sani cewa wa’adin sa zai zarce zagayen zaɓe ɗaya. Don haka ya yi duba ga muradun ƴan ƙasa, ba wai na waɗanda suka naɗa shi ba,” in ji sanarwar ADC.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook