A iya wata 1 a Najeriya, an kama masu laifi 1,950, an ceto 141, EFCC kuma ta ƙwato sama da naira biliyan 21

5

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) ta bayyana cewa a watan Agustan 2025, ƴan sanda sun kama mutane 1,950 tare da ceto mutane 141 da a kai garkuwa da su, yayin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci (EFCC) ta samu nasarar hukunce-hukunce 588 tare da ƙwato naira biliyan 21.06.

Wakilinmu ya tattaro daga bayanin da Daraktan Janar na NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, ya gabatar a taron manema labarai na haɗin guiwa a Abuja cewa, “Sakamakon na nuna nasarorin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, ingantaccen tsarin leƙen asiri da bayyananniyar sadarwa da jama’a.”

An kuma ce sojojin Najeriya sun aiwatar da ayyuka 261, sun ƙwace makamai da kashe ƴan ta’adda 30 a Zamfara, yayin da wasu 76 suka miƙa wuya.

Haka kuma, NDLEA ta kama mutane 944 kan laifin ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi, ta ƙwace kilo 66,255.81 na kayan maye, tare da samun nasarar hukunce-hukunce 17 a kotu, ciki har da na manyan dillalai biyu.

EFCC ta binciki shari’u 1,293 tare da ƙwato kuɗaɗe da dama, ciki har da dala miliyan 2, fam dubu 74,450 da Yuro 201,015, in ji NOA.

Leave A Reply

Your email address will not be published.