Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ɗaliban Jihar Jigawa sun yi fice a Gasar Karatun Al-Ƙur’ani Maigirma ta Najeriya karo na 40 da aka gudanar a Maiduguri, Jihar Borno, inda suka lashe manyan matsayai a rukunin mata, lamarin da ya ƙara jaddada jajircewar jihar wajen bunƙasa ilimin addinin Musulunci.
Honarabul Mohammed T. Mohammed (Sabo Ƴankoli), Mai Ba Gwamnan Jigawa Shawara na Musamman kan Ilimin Tsangaya, ne ya bayyana hakan a cikin saƙon taya murna da yabawa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Dr. Malam Umar Namadi.
“Ina miƙa saƙon taya murna ta ga Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa bisa gagarumar nasarar da jihar ta samu a wannan babbar gasa da aka gudanar a Maiduguri,” in ji Ƴankoli.
Ya kuma miƙa godiya ta musamman ga Babban Sakataren Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar Jigawa (Islamic Education Bureau – IEB), Dr. Mubarak Abdulwahab, da shugabanni da ma’aikatan hukumar, tare da al’ummar jihar baki ɗaya, bisa haɗin kai da jajircewar da suka nuna.
A cewar bayanan da TIMES HAUSA ta tattaro, Jihar Jigawa ta samu nasara a rukuni biyu, inda Mubaraka Adamu Idris ta lashe matsayi na farko a rukunin Haddar Hizifi Sittin (na mata), inda aka karrama ta da sabuwar mota, kujerar aikin Umarah, da kuma maƙudan kuɗaɗe na miliyoyin nairori.
Haka kuma, Khadija Muhammad Sani ta lashe matsayi na biyu a rukunin Haddar Al-Kur’ani Mai Girma tare da Tafsiri (na mata), inda ita ma ta samu kujerar Umarah da kuɗaɗe masu yawa na miliyoyin nairori.
Ƴankoli ya bayyana cewa wannan nasara hujja ce ƙarara ta irin zuba jari da Jihar Jigawa ke ci gaba da yi a fannin ilimin addinin Musulunci da na Al-Ƙur’ani, musamman ta hanyar gyare-gyaren tsangaya da makarantun addini.
“Ina taya murna ga zakarun gasar, malamansu, iyayensu da ɗaukacin al’ummar Jihar Jigawa. Allah Maɗaukakin Sarki Ya albarkaci ilimin da aka samu, Ya saka wa masu bada gudummawa da alheri, Ya kuma sanya wannan nasara ta zamo alheri ga jihar da al’ummar Musulmi baki ɗaya,” in ji shi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook