Abin da ya faru da jami’an sojan Najeriya 11 da Burkina Faso ta tsare bayan tattaunawar diflomasiyya
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
An saki jami’an sojojin Najeriya guda 11 da ke cikin jirgin sojan sama na C-130 da yai saukar gaggawa a Burkina Faso, bayan tsare su na tsawon kusan kwanaki tara kan zargin keta dokar sararin samaniyar ƙasar.
An tsare jami’an ne a makon da ya gabata daga hannun hukumomin Burkina Faso, bayan da suka ce jirgin ya karya dokokin sararin samaniyarsu.
TIMES HAUSA ta fahimci cewa an saki jami’an ne a daren Laraba, lamarin da kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar.
Ebienfa ya shaida wa manema labarai cewa an saki sojojin ne bayan wata babbar tawagar diflomasiyya daga Najeriya ta kai ziyara Burkina Faso.
Tawagar, wadda Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya jagoranta, ta gana da shugabannin gwamnatin Burkina Faso domin warware saɓanin da ya biyo bayan sauƙar gaggawar jirgin.
A wata sanarwa da kakakin ministan, Alkasim Abdulkadir, ya fitar, an ce ƙasashen biyu sun cimma matsaya cikin kwanciyar hankali.
“Cikin fahimta da tattaunawa mai ma’ana, gwamnatocin ƙasashen biyu sun warware matsalar da ta shafi matuƙan jirgin Sojan Sama na Najeriya da ma’aikatansa, lamarin da ya ƙarfafa amincewa da kuma nuna muhimmancin tattaunawa wajen magance lamurra masu sarƙaƙiya,” in ji sanarwar.
A baya, Ƙungiyar Kasashen Sahel (Alliance of Sahel States – AES), wadda ta haɗa da Nijar, Mali da Burkina Faso, ta zargi Najeriya da keta sararin samaniyar Burkina Faso.
Ƙungiyar ta ce sauƙar jirgin a birnin Bobo-Dioulasso da ke kudu maso yammacin Burkina Faso ya zama take ikon ƙasar.
Sai dai Rundunar Sojan Sama ta Najeriya (NAF) ta musanta zargin, tana mai cewa sauƙar jirgin ta kasance ne saboda matsalar tsaro da kuma “bin ƙa’idojin tsaron jiragen sama na ƙasa da ƙasa.”
NAF ta bayyana cewa matuƙan jirgin sun lura da wata matsalar na’ura da ta tilasta sauƙar gaggawa a filin jirgin sama mafi kusa, wato Bobo-Dioulasso, yayin da jirgin ke kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal.
A makon da ya gabata, Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce lamarin ba shi da alaƙa da duk wani tsoma bakin Najeriya a wani juyin mulki da aka samu a Benin.
Ya ce a wancan lokacin ana ci gaba da tattaunawa domin warware matsalar cikin lumana.
“Muna tattaunawa ne domin mu warware wannan lamari mai sarƙaƙiya cikin gaggawa. Ana tafiyar da komai ne ta hanyar diflomasiyya,” in ji Tuggar a lokacin.
TIMES HAUSA ta fahimci cewa sakin jami’an ya kawo karshen tashin hankalin diflomasiyyar, tare da sake jaddada muhimmancin tattaunawa tsakanin ƙasashen yankin Sahel da Najeriya.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook