Gwamna Namadi ya rantsar da sabbin masu ba shi shawara uku, ya jaddada riƙon amana da yi wa Jigawa aiki
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin Masu Ba Shi Shawara na Musamman guda uku, yana mai jaddada buƙatar yin aiki da gaskiya, sadaukarwa da ƙasƙantar da kai wajen hidimar al’umma da ci gaban jihar.
An gudanar da bikin rantsarwar ne da safiyar Talata a Zauren Majalisar Zartarwa na Fadar Gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.
Waɗanda aka rantsar sun haɗa da Alhaji Kabiru Hassan Sugungum, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Majalisar Tarayya; Ibrahim Ahmad Kwaimawa, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Dangantakar Ma’aikata (Industrial Relations); da kuma Ado Sani Birnin Kudu, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Aikin Gwamnati (Civil Service Matters).
Da yake jagorantar rantsarwar, Gwamna Namadi ya bayyana bikin a matsayin muhimmin mataki wajen ƙarfafa gwamnatinsa da kuma bunƙasa tafiyar da harkokin Jigawa.
“Yau mun ɗora wa waɗannan mutane nauyin da ke da matuƙar muhimmanci ga nasarar wannan gwamnati da kuma ci gaban Jihar Jigawa,” in ji gwamnan.
Ya bayyana cewa an zaɓi sabbin masu ba da shawarar ne bisa cancanta, mutunci, gogewa da kuma ƙwarewar da suka nuna a baya wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
“Masu Ba da Shawarar da muka rantsar a yau mutane ne masu cikakken mutunci, gogewa da kuma ƙwarewa da aka tabbatar da su. Tarihinsu da bayanan aikinsu sun nuna cewa su ƙwararru ne masu iya tafiyar da al’amura, kuma za su iya taka rawar gani wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati,” in ji shi.
Gwamnan ya tunatar da su cewa, aikin gwamnati amana ce, yana mai cewa rantsuwar da suka yi alƙawari ne mai ƙarfi a wajen Allah da al’ummar Jigawa.
“Duk da farin cikin da nake yi na taya ku murna, wajibi ne in tunatar da ku nauyin da wannan muƙami ke ɗauke da shi. Aikin gwamnati amana ce, kuma rantsuwar da kuka yi alƙawari ne mai tsarki a wajen Allah da mutanen Jigawa. Samun shugabanci girmamawa ce amma kuma babban nauyi ne,” in ji Namadi.
Ya buƙace su da su riƙa gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, jajircewa da nuna tawali’u, tare da fifita muradun Jigawa sama da na kansu.
“Ina roƙon ku da ku ci gaba da bayar da mafi kyawun gudummawarku kamar yadda kuka saba a baya. Ku yi aiki da niyya mai kyau, sadaukarwa da tawali’u, tare da fifita muradun Jigawa. Ina da yaƙinin Allah zai yi muku jagora ya kuma taimake ku,” in ji shi.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ba su hikima, ƙarfi da kariya, tare da yi wa gwamnatinsa gaba ɗaya jagora a ƙoƙarin da ake yi na bunƙasawa da ciyar da jihar gaba.
Da yake jawabi a madadin sauran sabbin masu ba da shawarar, Alhaji Kabiru Hassan Sugungum ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna musu.
Ya tabbatar wa gwamnan da samun cikakkiyar biyayya ga gwamnatinsa da Majalisar Zartarwa ta jihar, yana mai alƙawarin ba da gudummawa wajen aiwatar da Ajandar Muradu 12 ta gwamnatin Jigawa, daidai da Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Mun fahimci girman nauyin da aka ɗora mana, kuma da yardar Allah za mu yi aiki tuƙuru domin mu cancanci wannan amincewa, tare da tallafa wa hangen nesan gwamna na gina Jigawa mafi girma,” in ji Sugungum.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook