Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kai samame ofisoshi da gidajen tsohon Antoni Janar na Tarayyar Najeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, a Abuja da Jihar Kebbi.
An tabbatar da samamen ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Doka, ya fitar a ranar Laraba.
A cewar Doka, samamen ya biyo bayan ambaton da ofishin Malami ya yi na Babi na Tara na Rahoton Kwamitin Bincike na Shari’a na Ayo Salami.
Ya ce manufar samamen ita ce ƙwace Babi na Tara na rahoton, yana mai zargin Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, da nuna son kai, tare da neman ya janye kansa daga duk wani al’amari da ya shafi Malami.
Rahoton Ayo Salami da Rikici
Kwamitin Bincike na Ayo Salami, wanda aka kafa a 2021, ya binciki zargin cin hanci, amfani da muƙami ba bisa ka’ida ba da kuma sarrafa kadarorin da aka ƙwato a EFCC, musamman a zamanin Ibrahim Magu.
Kwamitin ya miƙa rahotonsa ga fadar shugaban ƙasa a Nuwambar 2021, amma ba a fitar da cikakken rahoton ga jama’a ba, sai wasu sassa kaɗan nasa.
TIMES HAUSA ta fahimci cewa Babi na Tara na rahoton ya ƙunshi bayanai da shawarwari kan rawar da wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ola Olukoyede, suka taka a lokacin da yake kula da EFCC.
Martanin Malami
Ofishin Malami ya bayyana samamen a matsayin “abin firgita matuƙa,” yana zargin cewa wani nau’i ne na tsoratarwa da ramuwar gayya.
Sanarwar ta ce an jefa lafiyar Malami da ma’aikatansa cikin haɗari, tare da jawo hankalin ƴan Najeriya da ƙasashen waje kan duk wani abin da ka iya faruwa.
Malami ya ƙalubalanci EFCC da ta bayyana dalilin doka na yin samamen, yana tambayar dalilin rashin bin ƙa’ida idan akwai gaskiya a binciken.
Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin farar hula, ƙwararru da masu kare haƙƙin ɗan Adam da su matsa wa gwamnati lamba domin fitar da cikakken rahoton Ayo Salami, musamman Babi na Tara.
“Ina shirye in tsaya gaban kotun da ta cancanta a cikin tsari na gaskiya,” in ji Malami, yana mai cewa samame da shari’ar kafafen yaɗa labarai ba za su maye gurbin bin doka ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da zargin na Malami ba.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook