ICPC ta samu nasarar shari’a kan wani Daraktan da yai ƙaryar shekarun haihuwa, ya karɓi albashi bayan ritaya

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Ma’aikatun Gwamnati (ICPC) ta samu nasarar gurfanar da tsohon Mataimakin Darakta na Ma’aikatar Noma da Bunƙasa Karkara ta Tarayya a Jihar Kwara, Dare Adebowale Oladapo, bisa laifin ƙirƙirar shekarun haihuwa da kuma karɓar albashi na watanni huɗu bayan lokacin da ya kamata ya yi ritaya ya yi.

TIMES HAUSA ta tattaro cewa an yi hukuncin ne a gaban Mai Shari’a Ibrahim Yusuf na Babbar Kotun Jihar Kwara da ke Ilorin, a ranar Talata, 7 ga Oktoba 2025, ƙarƙashin shari’a mai lamba KWS/64C/2022.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƙarar ta samo asali ne daga wani ƙorafi da lauya F. F. Ikebundu (Esq.) na Ayo Ajomole & Co., ya shigar a gaban ICPC, inda bincike ya gano cewa wanda ake tuhuma ya daɗe yana amfani da sabuwar shekarar haihuwa da ya ƙirƙira domin ƙara wa kansa shekarun aiki.

Takardun shari’ar sun nuna cewa lauyoyin ICPC, Kalu Ugbo da Zainab Moshood, sun shaida wa kotu cewa Oladapo ya karɓi albashi da alawus na Naira 1,233,258.95 daga 2019 zuwa 2020, duk da cewa ya wuce lokacin ritayarsa.

A cikin lissafin tuhume-tuhumen, an bayyana cewa ya canza shekarar haihuwarsa a Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Kasa (NPC), sannan ya yi rantsuwar ƙarya a takardar Affidavit da aka yi masa ranar 15 ga Fabrairu 2012, inda ya bayyana cewa an haife shi 11 ga Nuwamba 1964 maimakon ainihin shekarar haihuwarsa 11 ga Nuwamba 1959.

Wannan ya bashi damar sauya bayanan aikinsa tun daga 1997 lokacin da ya fara aiki a Ma’aikatar Noma da Bunƙasa Karkara ta Tarayya.

Kotun ta kuma saurari tuhumar da ta ce daga watan Disamba 2019 zuwa Afrilu 2020, Oladapo ya yi amfani da mukaminsa wajen karɓar albashi da alawus ba bisa ka’ida ba, bayan ya tsawaita shekarun aikinsa ta hanyar yaudara, abin da ya sabawa Sashe na 19 na Dokar ICPC ta 2000.

Bayan gabatar da shaidu, Mai Shari’a Yusuf ya same shi da laifi a kan tuhuma ta ɗaya da ta biyu, inda ya ce ya yi rantsuwar ƙarya da ƙoƙarin ba kansa fa’ida ta rashawa, bisa dokar ICPC ta 2000.

Sai dai kotu ta wanke shi daga tuhume-tuhumen tuhuma ta uku.

Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a kurkuku tare da zaɓi na biyan tarar ₦100,000 kan kowanne daga cikin tuhume biyu da aka same shi da laifi a kai.

Bugu da ƙari, kotun ta umarce shi da ya biya gwamnatin tarayya ₦1,233,258.95 da ya karɓa cikin watannin da ya wuce lokacin ritayarsa.

TIMES HAUSA ta gano cewa bayan hukuncin, Oladapo ya biya tarar ₦200,000 tare da mayar da cikakken adadin kudaden da ya karɓa ba bisa ka’ida ba a cikin asusun ICPC.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.