Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Wata tsohuwa mai shekara 69, Misis Kate Bosede Akomolafe, ta ɗauki hankulan mutane a yayin bikin karɓar sabbin ɗalibai (matriculation) na Cibiyar Karatu Ta Nesa (Distance Learning Centre) ta Jami’ar Ibadan, inda ta shiga cikin sabbin ɗalibai sama da 5,000 da suka ɗauki rantsuwa a ƙarshen mako.
TIMES HAUSA ta tattaro cewa, Registrar na jami’ar, Mista Ganiyu O. Saliu, ne ya gudanar da rantsuwar, inda sama da ɗalibai 5,000 suka shiga cikin shirin karatun nesa na jami’ar a fannonin karatu 16.
Hotunan bikin sun karaɗe kafafen sada zumunta, inda aka ga tsohuwar matar cikin farinciki sanye da rigar matriculation.
Wata sanarwa daga shafin jami’ar ta Facebook ta bayyana cewa Misis Akomolafe tsohuwar ma’aikaciyar kamfanin R.T. Briscoe Motors ce, yanzu kuma tana noma da kuma gudanar da ƙungiyar tallafawa jama’a (NGO).
“Ta shiga jami’a don yin karatun aikin zamantakewa (Social Work) domin inganta ayyukan ƙungiyarta,” in ji sanarwar.
An haifi Misis Akomolafe a ranar 22 ga Disamba, 1956, ta fara karatu a Government Secondary School, Creek Road, Port Harcourt inda ta sami takardar WAEC a 1976.
Bayan shekaru kusan 50, ta sake zana jarabawar WASSCE da NECO a 2023 domin cika burinta na yin digiri.
A wani jawabi, Mataimakin Shugaban Jami’a (ɓangaren gudanarwa), Farfesa Peter O. Olapegba, wanda ya wakilci Shugaban Jami’a, Farfesa Kayode O. Adebowale, ya shawarci sabbin ɗaliban da su kasance masu tsari da natsuwa a dukkan mu’amalolinsu.
“A gaskiya, nasara ta gaskiya tana zuwa ne daga zaɓin da mutumya aminta da shi. Ku tuna cewa ku ne kuke da alhakin nasararku a UI, inda ilimi da zamantakewa ke tafiya hannu da hannu,” in ji shi.
Farfesan ya kuma yi gargaɗi ɗaliban da su kiyaye dokokin jami’ar, yana mai cewa jami’ar ba za ta lamunci rashin ladabi ko halayen da zasu ɓata sunanta ba.
Ya ƙara da cewa nasarar ɗalibai ba kawai ta rubuce-rubuce za a auna ta ba, har da yadda za su yi tasiri ga al’umma bayan kammala karatunsu.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook