EFCC ta yi wa matasa nasiha, ta ce su bi shawararta ko nan gaba su yi nadama

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya shawarci matasan Najeriya da su guji aikata damfara ta yanar gizo tare da karkatar da basirarsu wajen aikin gina ƙasa da ci gaban tattalin arziƙi.

Rahotannin da wakilinmu ya tattara sun nuna cewa, Olukoyede ya bayar da wannan shawara ne a ranar Laraba, 8 ga Oktoba, 2025, a wajen taron bunƙasa ƙirƙira na matasa da yara mai taken “Future Innovator: Young Minds, Big Ideas, Creating Tomorrow Today”, wanda aka gudanar a ƙarƙashin Kids and Teens STEAM Innovate Buildathon Bootcamp, ga yara ƴan shekaru bakwai zuwa sha takwas.

A jawabin sa na musamman wanda Jami’in Hukumar EFCC mai riƙon muƙamin Darakta na Yankin Kaduna, Mataimakin Kwamanda Bawa Usman Kaltungo, ya karanta, Olukoyede ya jaddada muhimmancin guje wa ayyukan zamba da damfara, musamman ta intanet, yana mai cewa ya kamata matasa su yi amfani da hikimarsu da baiwar da Allah ya ba su wajen taimaka wa gwamnati da al’umma baki ɗaya.

“Ina ganin ana yawaita aikata munanan ɗabi’u a tsakanin matasa, amma ina roƙonku kada ku bi wannan hanyar. Ku guji shiga cikin damfarar intanet domin nan gaba za ku yi nadama. Ku yi amfani da lokacinku da tunaninku wajen samar da ayyukan da za su sa ku alfahari a gida da ƙasashen waje. Ku tuna cewa zamaninku ya bambanta da namu,” in ji shi.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.