Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ya ƙaddamar da sabbin injinan ruwa domin tabbatar da samar da tsaftataccen ruwa
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da sabbin injinan samar da ruwan sha masu ƙarfin KB 250 da KB 150, tare da gyaran babban injin Mahadi Kature da ke haɗe da babbar tashar ruwan sha ta yankin, domin magance matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar jama’a.
Shugaban ƙaramar hukumar, Builder Muhammad Uba ne ya bayyana hakan yayin miƙa injinan ga al’ummar yankin, inda ya ce ƙarancin ruwan sha zai zama tarihi a mulkinsa.
A cewarsa, “Za mu ci gaba da gyara da inganta dukkan kayayyakin samar da ruwa domin samar da mafita mai ɗorewa ga kowa da kowa.”
Wakilinmu ya fahimci cewa, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Yahuza Ibrahim Iggi, wanda shi ne mai kula da ɓangaren ruwan sha na yankin, ya jaddada cewa an samu ci gaba sosai a ɓangaren samar da ruwa a mulkin yanzu.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da manema labarai, Malam Sani Commander, ya ce wannan aikin zai magance matsalar da ta daɗe tana addabar garin Birnin Kudu.
Ya bayyana cewa jama’ar Dutsawa da Kantudu sun riga sun fara amfana daga aikin gyaran tashar ruwan sha ta Vocational wacce aka kammala kaso 80 cikin dari na aikinta.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook