Matatar Dangote ta dakatar da Sayar da man fetur da naira, za a iya samun canjin farashin litar mai a Najeriya
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Masana’antar Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals ta sanar da dakatar da sayar da man fetur da Naira daga ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.
Rahoton da wakilinmu ya tattaro ya nuna cewa, sanarwar ta fito ne daga Sashen Harkokin Kasuwanci na Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals, inda aka shawarci dukkan abokan hulɗar kamfanin da suka riga suka biya da naira su nemi a mayar musu kuɗaɗensu.
Sanarwar ta ce: “Muna shaida muku cewa Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ya yi amfani da fiye da rabon da ya samu na ɗanyen mai a naira, saboda haka ba za mu iya ci gaba da sayar da man fetur da naira ba. Wannan mataki zai fara aiki daga ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, kuma za mu ba da ƙarin bayani kan lokacin da za a ci gaba da sayarwa (da naira) bayan an warware lamarin.”
Wakilinmu ya fahimci cewa, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a watan Yulin 2024 ta umarci kamfanin NNPC Ltd ya tattauna da Dangote da sauran matatun man cikin gida domin tabbatar da sayar da ɗanyen mai a naira, tare da sharuɗɗan cewa duk wani samfurin da aka tace a cikin gida za a sayar da shi ga kasuwar cikin gida da naira.
Sai dai masana’antar Dangote ta taɓa dakatar da irin wannan sayarwa a watan Maris 2025 saboda bambancin da ke tsakanin kuɗaɗen da take samu da kuma farashin ɗanyen man da ake saye da dala.
A watan Afrilu, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tsarin sayar da mai da samfuransa da Naira ba wani lokaci na ɗan gajeren lokaci ba ne, illa mataki na dindindin domin tallafa wa tace mai a cikin gida da kuma rage dogaro da kuɗaɗen waje.
Masana sun ce dakatarwar na iya janyo tasiri ga farashin man fetur a cikin gida muddin ba a samu sulhu da wuri ba.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook