Kano ce jiha mafi cin jarrabawar NECO a 2025, Gwamna Abba ya nuna farin cikinsa

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin cikinsa bayan da Jihar Kano ta zama jiha mafi samun nasara a jarrabawar NECO ta 2025 ga ɗaliban makarantu, inda ta zarce sauran jihohi a sakamakon ƙarshe.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya ce wannan nasara ta samu ne sakamakon gyare-gyare da zuba jari da gwamnatinsa ta zuba a fannin ilimi.

Ya ce, “Alhamdulillah! Wannan nasara ta fito daga mayar da hankali a fannin ilimi da kuma jarin da muka zuba a ɓangaren malamai, ɗalibai da makarantu. Wannan nasara ce ta kowa da kowa – malamai, ɗalibai da iyaye.”

Binciken wakilinmu ya gano cewa Shugaban NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi, ne ya bayyana sakamakon a taron manema labarai da aka gudanar a Minna, Jihar Neja.

A cewarsa, Kano ta yi fice da ɗalibai 68,159 waɗanda suka samu credits biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, wanda ya kai kashi 5.02% na ɗaliban ƙasa baki ɗaya.

Lagos ta biyo baya da ɗalibai 67,007, yayin da Oyo ta zo na uku da ɗalibai 48,742.

A jimlace, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, inda 818,492 (kashi 60.26%) suka samu credits biyar da Turanci da Lissafi, yayin da 1,144,496 (kashi 84.26%) suka samu credits biyar a sauran darusa.

Wakilinmu ya tattaro daga gwamnatin Kano cewa nasarar ta samo asali ne daga shirye-shiryen da suka haɗa da bayar da kayan makaranta kyauta, gyaran ajujuwa da samar da kayan koyo, ɗaukar sabbin malamai da horar da su, da kuma samar da tallafin karatu da ɗaukar nauyin karatun ƴaƴan jihar a manyan makarantu.

Wata masaniyar harkokin ilimi a Kano, Dokta Amina Lawal, ta shaida wa manema labarai cewa wannan nasara ta Kano na da ma’anar gaske ga sauran jihohi.

Ta ce, “Kano ta kafa sabon matakin da sauran jihohi za su dinga koyi da shi. Wannan ya nuna muhimmancin shugabanci na hangen nesa da kuma zuba jari mai ɗorewa a ilimi.”

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.