Mustapha Sule Lamido ya taya Farouk Gumel murna kan naɗinsa a matsayin Shugaban Hukumar Alkinta Arziƙin Botswana

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Mustapha Sule Lamido, ya bayyana jin daɗinsa kan naɗin da aka yi wa ɗan Najeriya, Farouk Mohammed Gumel, a matsayin Shugaban Daraktocin Hukumar Alkinta Arziƙin Ƙasar Botswana (BSWF).

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mustapha Lamido ya ce wannan naɗin ya tabbatar da ƙwarewar Gumel da tarihin aikinsa mai inganci, tare da nuna irin ƙwazon da ƴan Najeriya ke da shi a matakin duniya.

Ya ce, “Na yi farin ciki matuƙa da wannan naɗin. Ba wai kawai ya nuna tarihin aikinsa bane, har ma ya tabbatar da cewa ƴan Najeriya na iya taka muhimmiyar rawa a matakin ƙasa da ƙasa. Ina yi masa fatan alheri da addu’ar samun nasara.”

Binciken wakilinmu ya nuna cewa Farouk Mohammed Gumel ya shahara wajen nuna ƙwarewa a fannoni daban-daban na tattalin arziƙi da shugabanci.

Ƙwaƙƙwarar nasarar da ya samu a baya ta sanya shugaban ƙasar Botswana, Duma Gideon Boko, ya ba shi wannan babban matsayi a ƙasarsa.

Masu lura da harkokin gwamnati sun bayyana cewa wannan naɗin ba abin mamaki ba ne, la’akari da irin rawar da Gumel ya taka a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya yi aiki a muhimman muƙamai.

Gumel ya yi karatun digiri na farko da ya kammala da sakamako na First Class a fannin Materials Technology, sannan ya samu digiri na biyu a fannin Clean Technology da matakin Distinction daga jami’o’i a Birtaniya.

Haka kuma, yana da gogewa a manyan kamfanoni na ƙasa da ƙasa ciki har da PwC, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin lissafin kuɗi da shawara a duniya.

Haka kuma, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Nigerian Sovereign Investment Authority (NSIA), inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da asusun arziƙin Najeriya a wani mawuyacin lokaci na tattalin arziƙin ƙasa.

Masana sun bayyana cewa zuwan Gumel a matsayin shugaban BSWF alama ce ta zamanin da ake ciki na Industrial Revolution na huɗu (4IR), wanda ake buƙatar ƙwarewa da fasaha fiye da takardun shaidar karatu kawai.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.