Fubara ya koma bakin aiki bayan wata shida na dokar ta-ɓaci a Rivers, dubannan mutane ne suka tarbe shi a Fadar Gwamnati
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, sun koma kujerunsu na mulki yau Alhamis, bayan shafe watanni shida a waje, sakamakon dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaƙaba a jihar a ranar 18 ga Maris, 2025.
Wakilinmu ya tattaro daga majiyoyi da dama cewa a daren Laraba, tsohon mai riƙon muƙamin gwamnan jihar, tsohon hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (rtd), ya miƙa ragamar mulki ta cikin jawabin ƙarshe da ya yi wa jama’a.
A cikin jawabin, Ibas ya shawarci manyan ƴan siyasar jihar da su rungumi mutunta juna da tattaunawa domin kauce wa sake faɗawa cikin rikici.
Tun bayan rantsar da Fubara a matsayin gwamna a watan Mayun 2023, rikici ya kunno kai tsakaninsa da tsohon gwamna kuma yanzu Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, kan ikon siyasar jihar.
Lamarin ya rikiɗe zuwa rikici tsakanin majalisar dokoki da fadar gwamnatin jihar, wanda daga ƙarshe ya sa Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar mai arziƙin mai.
A cikin watan Yuni, Shugaba Tinubu ya gana da Fubara, Wike da shugaban majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, inda aka samu alamun sulhu tsakanin manyan ƴan siyasar.
Haka kuma an ga Fubara da Wike tare a wasu bukukuwa a jihar, abin da ya ƙara tabbatar da warwarewar rikicin a zahiri.
Duk da haka, wakilinmu ya gano cewa yayin mulkin riƙon ƙwarya, Admiral Ibas ya ƙaddamar da hukumar zaɓe ta jihar (RSIEC) a watan Yuli, wadda ta gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a ranar 30 ga Agusta.
Sakamakon ya nuna jam’iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20, yayin da PDP ta samu nasara a uku.
Shugaba Tinubu ya bayyana a jawabin da ya yi a ranar Laraba cewa ayyana dokar ta-ɓaci a watan Maris ya zama dole domin kauce wa taɓarɓarewar tsaro da rikicin siyasa da zai iya rikiɗewa zuwa mummunar gaba.
Duk da haka, shugaban ya tabbatar da cewa shugabannin jihar sun dawo bakin aiki tare da dubban al’umma da suka fito da farin ciki domin tarbar su a gidan gwamnati.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook