Gwamnatin Najeriya ta raba naira biliyan 330 ga wasu talakawa, na saura na kan hanya – Wale Edun
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta raba naira biliyan 330 ga talakawa da marasa galihu a faɗin ƙasar nan ta hannun hukumar kula da tsarin tallafin jama’a, wato National Social Safety-Net Coordinating Office (NASSCO).
Ministan Kuɗi kuma mai Tsara Tattalin Arziƙin Ƙasa, Wale Edun ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron kwamitin musamman na shugaban ƙasa kan shirin tallafin zamantakewa.
Edun ya ce shirin tallafin zamantakewar da aka samar domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa ya koma kan turba yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa gidaje miliyan 19.7, da ke wakiltar mutane sama da miliyan 70, sun samu shiga cikin National Social Register.
Ya ƙara da cewa an riga an biya gidaje miliyan 8.5 a ƙalla sau ɗaya, inda kowanne gida ya karɓi naira 25,000.
Wasu kuma sun karɓi biyan sau biyu ko uku, yayin da sauran gidaje miliyan 7 za su samu kuɗinsu kafin ƙarshen shekara.
Wakilinmu ya fahimci cewa kuɗaɗen an samo su ne daga dalolin Amurka miliyan 800 da Bankin Duniya ya bayar a matsayin tallafi ga Najeriya.
Ministan ya ce tsarin an gina shi ne bisa ingantacciyar hanya, inda aka tabbatar da cancantar waɗanda za su amfana ta hanyar lambar katin ɗan ƙasa (NIN), sannan ana tura kuɗaɗen ta bankuna ko kuma ta lalitar wayar salula.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook