Dangote ya ce, direbobin tankunansa na samun albashi fiye da na ma su digiri a Najeriya
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa direbobin kamfaninsa na samun albashi mai tsoka, wanda ya fi na yawancin masu digiri a Najeriya.
Wannan jawabi na Dangote ya fito ne a wani faifan bidiyo da tashar TVC ta yaɗa a shafinta na X ranar Talata, inda ya maida martani kan zargin da ƙungiyar NUPENG ta yi masa da abokinsa Sayyu Dantata.
Zargin NUPENG
Ƙungiyar ta NUPENG ta yi zargin cewa Dangote na ƙoƙarin mamaye harkar rarraba man fetur ta hanyar shigo da sabbin motocin CNG daga Matatar Dangote, tare da tilasta wa direbobi su sanya hannun cewa ba za su shiga kowace ƙungiya ta ma’aikata ba.
A baya dai ƙungiyar ta ce za ta fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya tun daga 8 ga Satumba domin nuna adawa da abin da ta kira “cin zarafin ma’aikata.”
Ƙungiyar ma su motocin haya (NARTO) da kuma Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) sun nuna goyon bayansu ga NUPENG, inda shugaban NLC, Joe Ajaero, ya zargi Dangote da “cin moriyar ma’aikata tare da tauye musu haƙƙoƙinsu na doka.”
Martanin Dangote
A cikin bidiyon, Dangote ya musanta zargin, inda ya ce shirin kamfaninsa zai samar da ayyukan yi sama da 24,000, kuma direbobi za su iya samun rancen gidaje bayan shekaru biyar na aiki ba tare da matsala ba.
“Motocinmu ba za su yi aiki da robot ba. Kowacce mota na da ma’aikata shida, wanda hakan zai samar da ayyuka dubbai. Direbobinmu na samun albashi ruɓi uku zuwa huɗu fiye da mafi ƙarancin albashi a ƙasa. A gaskiya, wasu daga cikinsu na samun fiye da yawancin na masu digiri,” in ji shi.
Dangote ya kuma ƙara da cewa shiga ƙungiyar NUPENG ba dole ba ne, “Babu wanda ya hana su shiga ƙungiya. Amma shiga dole ba gaskiya ba ne. Muna so a dinga zaɓin shiga bisa son rai, ba tare da tilastawa ba.”
Wakilinmu ya fahimci cewa lamarin ya ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙwadago da kamfanin Dangote, yayin da ake jiran ganin ko NUPENG za ta ci gaba da matsa lamba ta hanyar yajin aiki ko kuma za a ci gaba da tattaunawa don sasanta rikicin.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook