Gwamna Namadi ya taya Farouk Gumel murnar samun shugabancin Asusun Kuɗaɗen Botswana
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya taya Farouk Mohammed Gumel murnar naɗinsa a matsayin Shugaban Asusun Kuɗaɗen Ƙasar Botswana (Sovereign Wealth Fund).
A wata sanarwa daga Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, a ranar Talata, 16 ga Satumba, 2025, gwamnan ya bayyana naɗin a matsayin hujjar ƙwarewar Farouk Gumel a harkokin kuɗi, noma da zuba jari a matakin ƙasa da ƙasa.
“Wannan naɗi ya nuna ƙima da mutuncin Jigawa a idon duniya. Muna alfahari da shi, kuma muna da tabbacin zai yi nasara wajen tafiyar da wannan muhimmin aiki,” in ji Gwamna Namadi.
Ya kuma yi alƙawarin addu’o’i da goyon baya daga gwamnati da al’ummar jihar, yana mai cewa nasarar Gumel ta zama alfahari ga Najeriya da Afirka baki ɗaya.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook