Ƴan sanda sun cafke ƙananan yara da matasa masu safarar miyagun ƙwayoyi, satar babura da fasa gidaje a Jigawa

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta cafke wasu mutane da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, satar babura da kuma fasa gidaje a wurare daban-daban na jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ya fitar ranar Asabar, an bayyana cewa an ƙwato babura guda biyu, miyagun ƙwayoyi, kayan ado da kuma kuɗaɗe daga hannun waɗanda ake zargi.

Fasa gidaje da sata

A ranar 9 ga Satumba, tawagar sintiri daga sashen Yalwawa ta cafke matasa takwas masu shekaru tsakanin 11 da 17, bayan karɓar wani ƙorafi da wani mutum ya kai.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Mubarak Musa (shekara 16), Abdulkadir Abubakar (shekara 17), Aliyu Isah (shekara 17), Adamu Usman (shekara 15), Benedict Joseph (shekara 14), Lucky Yuguda (shekara 15), Abubakar Idris (shekara 13), da Abdulwahab Idris (shekara 11), duk daga unguwannin Yalwawa da Sabuwar Takur a Dutse LGA.

A yayin bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma an ƙwato kayan da suka sata daga hannunsu.

Kama miyagun ƙwayoyi

Daga ranar 8 zuwa 12 ga Satumba, rundunar ta kai samame a Taura, Gwaram, Gujungu da Babura inda aka kama mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Abubuwan da aka kwato sun haɗa da:

  • Ɗaurin ganyen wiwi 34,
  • Ƙwayoyin D5 guda 1,500,
  • Ƙwayoyin Exol 960,
  • Kwalaben roba na ruwan maye 76,
  • Kwalaben suck and die 19,
  • Ƙwayoyin tramadol 13,
  • Kapsul ɗin Prega lump 6,
  • Kuɗi ₦12,100.

Waɗanda ake zargi, waɗanda shekarunsu ke tsakanin 14 da 29, sun amsa cewa suna safarar miyagun ƙwayoyi a Jigawa da maƙwabtan ƙananan hukumomi.

Satar babura

A ranar 7 ga Satumba, jami’an ƴan sanda daga Hadejia sun cafke wani Haruna Garba (28) ɗan Ƙaramar Hukumar Birniwa da babur ɗin Hajour UD mai launin fari, wanda darajarsa ta kai ₦750,000.

Daga baya wani Muhammad Sani daga Fadar Sarkin Hadejia ya bayyana kansa a matsayin mamallakin babur ɗin.

Wanda ake zargi ya amsa laifinsa, kuma an gurfanar da shi a kotu.

Haka kuma a ranar 6 ga Satumba, wani mazaunin Ringim ya kai ƙara cewa an sace masa babur ɗin Boxer.

Sintiri ya kai ga samo shi a Zakirai, Jihar Kano, tare da kama mutane biyu, Auwalu Adamu (25) da Audu Ilu (23).

Bincike ya kai ga kama abokan harkarsu Mustapha Yunusa da Sani Abubakar, waɗanda aka bayyana a matsayin sanannun masu satar babura da aka saki kwanan nan daga gidan yari.

SP Shiisu ya tabbatar da cewa bincike na ci gaba a sashen binciken manyan laifuka na Dutse a Jigawa, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.