Dubban mutane sun mamaye titunan Auckland suna kira da a ƙaƙaba wa Isra’ila takunkumi

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Fiye da mutane dubu hamsin sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa da ƙin jinin Isra’ila a birnin Auckland na New Zealand, a cewar ƙungiyar Aotearoa for Palestine, wacce ta shirya zanga-zangar.

Sai dai ƴan sanda sun ƙiyasta adadin masu halartar a matsayin adadin da ya kai kusan dubu 20, ba dubu 50 ba.

Masu zanga-zangar sun ɗauki tutar Falasɗinu tare da rubuce-rubucen da ke kira ga gwamnati ta ƙaƙaba takunkumi kan Isra’ila.

“Ba za mu amince a al’ada da kisan ƙare dangi ba,” in ji wani rubutu da aka riƙa ɗauka a lokacin zanga-zangar.

Ƙungiyar Aotearoa for Palestine ta yi kira ga gwamnatin haɗin gwiwa ta New Zealand ta ɗauki matakin ƙaƙaba takunkumi kan Isra’ila a matsayin goyon baya ga al’ummar Palasɗinu.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.