SULHU DA ƳAN TA’ADDA: Gazawa ce ga tsaron Najeriya da tsantsar rainin wayo ga arewacin Najeriya 

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Daga: Ahmed Ilallah

Kullum in na yi duba da ta’addancin da ke faruwa ga Arewa, musamman ta Yamma na kan tuna da wata magana ta Marigayi Sheikh Abubakar Gumi na kuma yi zurfin tunani a kan batun tsohon Gwamnan Edo Senator Adams Oshomole da kuma maganar da Gwamnan Jihar Zamfara na yanzu Garba Lawan Dare suka yi.

Me yasa Jihar Zamafara ta zama matattara ta da kuma focal point na ƴan ta’adda ko yan fashin Daji? Shin akwai wata manufa mai karfi a kan assasa wanan fitina a Zamfara da Arewacin Nigeria? Shin a kwai wani arziƙi da wasu haɗamammu ke amfana da shi, kuma suke ci gaba da assassa wannan fitina don biyan buƙatar kansu.

Na tuna kuma na ƙara tunani a kan wata Magana da Marigayi Sheikh Abubakar Gumi ya faɗa a cikin littafin sa mai suna (Where I Stand), Malam yana faɗin cewa “Bayan ya gama karatun sakandare a Makarantar SIS ta Kano, an turashi Makarantar Sakandare da ke Maru (Teachers College Maru), tun a wannan lokacin yana ganin Turawa suna yawan shiga waɗannan dazukan wannan ƙauyukan, amma ya rasa me suke zuwa dubawa ko nema….

To wannan kaɗai ya isa mutanen Arewa da Zamafara masu kishi su koma su yi nazarin a kan wannan magana da wannan bawan Allah, domin shi waliyi ne a nawa ra’ayin.

Magana a kan batun tsohon Gwamnan Jihar Edo Senator Adams Shomale a wani video da yake yawo a social media na wani kwamati na Majalissar Dattijai, yana faɗin cewa lokacin yana gwamna, ya kafa kwamati a kan rashin tsaron da ya mamaye Arewa da Jihar Zamfara wanda ya ke neman shiga kudancin Nigeria.

Adams Oshomole yace kwamitin ya gano irin dimbin arziƙin gold da ya mamaye wanna jihar kuma ya malala har zuwa jihohin kudu irin su Edo.

Ya nuna cewa wasu manyan ƙasar nan ne suke haƙar wannan arziƙi kuma a kitsa wanna fitinar da bawa wannan ƴan ta’adda makamai suna ta’addanci, su kuma suna cin karensu babu babbaka.

Abin takaicin yace wanna ruhoto nasa har tsohon Shugaban kas Marigayi Buhari ya kaiwa amma har yau babu wani abu da akayi a kan wannnan batu.

A kwannan Magana mai tada hankali itace maganar gwamnan Gwamnan Zamfara na yanzu, wanda a yanzu yace yana na na’urorin da suke nuna masa duk inda wannan yan ta’adda suke, amma ko ya sanar da jami’an tsaro basa daukan mataki a kai.

A wannan lokaci da a ke neman wai a yi sulhu da yan ta’adda, ya kamata hankalin mai yankan kaba ya koma ga hannun sa.

Duk mai hankali yasan cewa a shekaru sama da goma da wannan yankin ya shiga na rashin tsaro, talauci da rushewar tarbiya, gwamnatocin baya da yau basu maida hankali na kawo karshen wannan matsala ba.

Tsananin renin hankaline ga mutanen wannan yankin a ce an kasa fahimtar wannan matsalar da kuma samawa wannan yankin zaman lafiya.

alhajilallah@gmail.com

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.