Buji a Jigawa za ta ɗauki sabbin ƴan vigilante 40 domin ƙarfafa tsaro

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Ƙaraman Hukumarm Buji a Jihar Jigawa ta sanar da shirin ɗaukar sabbin jami’an vigilante guda 40 domin ƙara ƙarfi ga ayyukan tsaro a yankin.

Wakilinmu ya gano daga wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƙaramar hukumar, Aliyu B. Safiyanu, ya fitar ranar 11 ga Satumba, cewa Shugaban Ƙaramar Hukumar, Hon. Najib Falalu Tukur ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin kwamandan rundunar vigilante ta Jihar Jigawa, Alhaji Umar Salisu.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce gwamnatin Buji za ta ci gaba da tallafa wa vigilante, tare da ƙara musu alawus yayin da tattalin arziƙin yankin ke samun bunƙasa.

Ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa sadaukarwarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A nasa jawabin, Alhaji Umar Salisu, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa tallafin da yake bai wa rundunar, sai dai ya roƙi ƙarin taimako ta hanyar ba su motocin sintiri domin gudanar da aikin tsaro a dukkan gundumomi goma na ƙaramar hukumar.

Hon. Najib Tukur ya kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da yin aiki tare da vigilante domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Buji.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.