Wasu da ake zargin matsafa ne sun farmaki wajen jana’iza, sun hallaka mutane

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

An samu mummunan hari a daren Alhamis lokacin da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne suka kai farmaki wajen jana’iza a ƙauyen Ezi, Ogidi, ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa, Jihar Anambra, inda suka kashe mutane huɗu tare da jikkata wasu 15.

Shaidun da aka tattauna da su a wajen sun bayyana cewa, maharan sun iso ne a kan babura, suka buɗe wuta kan taron jama’a yayin da ake gudanar da bukukuwan jana’izar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro daga sashen Ogidi sun hanzarta zuwa wurin, sun dawo da doka da oda, tare da kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

“Binciken farko ya nuna cewa rikicin ƙungiyoyin asiri ne ya haddasa kai wannan hari. An samu ƙwararan hujjoji da harsasai guda 16 a wurin,” in ji Ikenga.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sanda na jihar, Ikioye Orutugu, ya la’anci lamarin tare da tabbatar wa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da shawo kan miyagun laifuka.

Wannan hari ya zo ne watanni bayan wani irin farmakin a Ihiala, inda mutane bakwai suka rasa rayukansu, ciki har da jami’an tsaro, a lokacin shirye-shiryen wani bikin jana’iza.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.