Gwamnan Kano ya aika da ƙudirin ƙara tsaurara dokar hana auren jinsi da sauran ayyukan masha’a a jihar

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da miƙa ƙudirin doka zuwa Majalisar Dokokin Jiharsa domin haramta auren jinsi da sauran abubuwan da aka bayyana a matsayin na rashin tarbiyya a jihar.

Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa, ya fitar ranar Juma’a, cewa gwamnan ya ba da amincewar ne a yayin taron majalisar zartarwa na 31 da aka gudanar a Kwankwasiyya City.

Tun farkon shekarun 2000 lokacin da aka aiwatar da tsarin shari’ar Musulunci a Kano da wasu jihohi na Arewa, gwamnatoci sun kasance masu ɗaukar tsauraran matakai kan batutuwan da suka shafi ɗabi’a da addini.

Duk da cewa Najeriya tuni tana da dokar hana auren jinsi tun shekarar 2014, jihar Kano ta sha nuna buƙatar ƙara tsaurara doka bisa koyarwar shari’a.

“Babu wata hanya da za mu bar abin da ya saɓawa addini da al’adunmu ya samu tushe a Kano. Wannan gwamnati tana da alhakin kare ɗabi’a da mutuncin al’ummarmu,” in ji Gwamna Yusuf.

Wakilinmu ya gano cewa ƙudirin zai hana auren jinsi da kuma wasu ɗabi’un da aka fi sani da maɗugo da luwaɗi a jihar, wanda gwamnati ta ce duka haramun ne.

Idan majalisar ta amince, masu aikata laifukan za su fuskanci tsauraran hukunci.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.