HASASHEN YANAYI: NiMet ta fitar da gargaɗi kan samun ruwan sama mai iska a yankunan Arewa da Kudu a yau Alhamis
Hukumar hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta bayyana hasashen yanayin yau Alhamis, 11 ga Satumba 2025, inda ta yi gargaɗi kan samun ruwan sama da ake sa ran zai biyo da iska mai ƙarfi a wasu sassan ƙasar.
Rahoton da wakiliyarmu ta tattaro daga NiMet ya nuna cewa a Arewa, da safe, ana sa ran samun guguwar iska da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu sassan jihohin Taraba da Adamawa.
Daga rana zuwa dare kuwa, za a samu ruwan sama haɗe da guguwa a jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Gombe da Bauchi.
A tsakiyar ƙasar kuwa, hasashen ya nuna za a tashi da gajimare tare da ɗan hasken rana a wasu wurare, da yiwuwar samun ɗan ruwan sama a Benue.
Daga bisani da rana, ana sa ran samun guguwar iska da ruwan sama mai ƙarfi a Nasarawa, Plateau, Kogi, Benue da Abuja.
A yankin Kudu kuma, rahoton ya ce akwai yiwuwar samun ɗan ruwan sama da safe a Akwa Ibom da Cross River, yayin da daga rana zuwa dare ake sa ran samun ruwan sama mai yawa a jihohin Osun, Oyo, Ekiti, Enugu, Anambra, Ebonyi, Abia, Imo, Delta, Edo, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.
NiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan yayin da ake ruwan sama saboda yiwuwar tasowar iska, wacce ka iya rage hangen hanya, sa tituna su zama masu matsala, da kuma kawo cikas ga ayyukan waje.
Haka kuma, an buƙaci al’umman da ke zaune a wuraren da ake fama da ambaliya da su kasance cikin shiri.