Rahoton ƙwararren masani kan yaƙi da ta’addanci da samar da tsaro, Zagazola Makama, ya nuna cewa, aƙalla mutane uku aka yi garkuwa da su a lokacin sallar asuba a masallacin Yarlaluka, Dansadau, a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Rahoton ya bayyana cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka mamaye masallacin a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:55 na safe yayin da jama’a ke cikin sallar asuba, inda suka yi awon gaba da mutane uku.
Wannan harin ya faru ne ƴan kwanaki bayan wani hari makamancin haka a masallaci a Ƙaramar Hukumar Patigi ta Jihar Kwara, inda aka harbe wani mai ibada da ya yi ƙoƙarin tsallakewa daga yin garkuwa da shi har lahira.
Yawaitar hare-hare a wuraren ibada na ƙara jefa tsoro a zuƙatan jama’a tare da sabunta kira ga gwamnati ta ƙarfafa matakan tsaro domin kare rayuka.
Rahoton ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro daga rundunar ƴan sanda da sauran hukumomi sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru, inda aka kuma samu rahotannin da ba a tabbatar ba cewa, an kama mutum shida da ake zargi da hannu a harin.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya shaida wa wakilin PUNCH cewa, “Ina cikin aiki. Zan kira ku daga baya.”
Sai dai har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoto, bai kira ba, bai kuma amsa saƙon WhatsApp da aka aika masa ba.
Irin wannan hari ya faru a wasu jihohin arewa maso yamma.
A Jihar Katsina, an kashe aƙalla masu ibada 27 tare da jikkata wasu da dama, bayan ƴan bindiga sun kutsa cikin masallaci a Unguwar Mantau, Ƙaramar Hukumar Malumfashi, inda suka buɗe wuta kan jama’a yayin sallar asuba.