SUBEB ta Jigawa ta buɗe ƙofar neman aikin zama Sakataren Ilimi na ƙaramar hukuma a jihar

39

Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Jigawa (SUBEB) ta sanar da buɗe shafin neman aikin Sakataren Ilimi a fadin ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da aka rarraba a madadin Shugaban Hukumar cewa, an buɗe wannan dama ne ga duk wanda ke da ƙwarewa da sha’awar bayar da gudummawa ga ci gaban harkar ilimi a jihar.

A cewar sanarwar, wanda zai nema dole ne ya kasance yana da B.Ed. (digiri na Bachelor of Education) tare da aƙalla shekaru 10 na ƙwarewa a aiki, ko NCE (Nigeria Certificate in Education) da aƙalla shekaru 18 na ƙwarewa.

Shafin neman zai fara aiki daga Litinin, 8 ga Satumba, 2025, kuma za a rufe shi da tsakar daren a Lahadi, 15 ga Satumba, 2025.

Za a iya nema ne kaɗai ta shafin yanar gizo ta hanyar ziyartar shafin: www.esrecruitment.subebjigawa.org.ng.

Leave A Reply

Your email address will not be published.