Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta bayyana hasashen yanayi na ranar Talata, 9 ga Satumba, 2025, inda aka yi gargaɗin yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi, hadari mai duhu, da yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan Najeriya.
Wakiliyarmu, Maryam Ayuba Auyo, ta tattaro daga rahoton da aka fitar ranar Litinin cewa, a Arewa, ana sa ran samun ruwan sama mai tsanani tare da hadari a safiyar wasu jihohi kamar Taraba, Adamawa, Kebbi, Zamfara, Gombe, Bauchi, Kaduna, Sokoto da Katsina, yayin da a yammacin yau irin wannan yanayi zai ratsa Borno, Sokoto, Kebbi, Bauchi, Kaduna, Adamawa, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara da Taraba.
A tsakiyar ƙasa kuma, rahoton ya nuna ana sa ran samun ruwan sama mai sauƙi da safe a Abuja, Kwara, Benue, Niger da Kogi, sannan da yamma ana hasashen samun hadari da ruwan sama mai tsanani a Nasarawa, Niger, Plateau, Kogi, Kwara, Benue da Abuja, inda aka yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya musamman a Niger da Kogi.
A Kudanci kuwa, rahoton ya ce za a sami girgizai da ruwan sama mai sauƙi da safe a wasu sassan Ebonyi, Imo, Abia, Oyo, Ogun, Edo, Lagos, Cross River da Akwa Ibom, yayin da da yamma ake sa ran samun ruwan sama matsakaici a mafi yawan yankin.
NiMet ta shawarci jama’a su kula da samun iska mai ƙarfi, yanayin hazo, da rashin gani sosai da zai iya kawo cikas a kan tituna da rage tsaron ababen hawa, musamman ga al’ummomin da ke zaune a yankunan da ake hasashen samun ambaliya.