Tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai ya sauya sheƙa zuwa ADC a Jigawa, ya yi alƙawarin yaƙar APC

42

A ranar Asabar, jam’iyyar ADC reshen Ƙaramar Hukumar Hadejia a Jihar Jigawa ta karɓi tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai, Hon. Baffa Saleh, wanda a baya ya tsaya takara a jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 da nufin neman wakiltar mazaɓar Hadejia/Auyo/Kafin Hausa.

Wakilinmu ya tattaro cewa Hon. Baffa Saleh ya fara da karɓar katin zama ɗan jam’iyyar ADC daga shugaban kwamitin tuntuɓa na mazabarsa, Hon. Binyaminu Ibrahim Excellency.

Da yake jawabi, Baffa Saleh ya ce: “Na shigo ADC ba don neman kujerar zaɓe ba, sai don bayar da gudummawa wajen ceto al’umma daga hannun wannan azzalumar jam’iyyar mai mulki, APC, wadda ke azabtar da jama’a.”

Shugaban kwamitin tuntuɓa na Hadejia, Malam Zakar T. Barde, ya halarci bikin tare da manyan ƴaƴan jam’iyyar a yankin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.