Rundunar ƴan sanda ta ragargaji manyan dillalan miyagun ƙwayoyi a Jigawa
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane goma sha uku da ake zargin manyan dillalan miyagun ƙwayoyi ne, a wani jerin samame da ta gudanar a sassan jihar daga ranar 2 zuwa 6 ga Satumba, 2025.
Wakilinmu, Zulkifl Abdullah ya tattaro daga sanarwar da SP Shiisu Lawan Adam, Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ya fitar, cewa samamen an shirya shi ne bisa sahihan bayanan sirri game da ayyukan masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran masu tayar da hankalin jama’a.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an rundunar daga sassa daban-daban ciki har da Dutse, da Guri, da Birnin Kudu, da Bamaina, da Babura da Roni, sun gudanar da samame kan maɓoyar masu laifin da wuraren da ake gudanar da safarar miyagun ƙwayoyi, inda aka kama mutane 13 waɗanda suka haɗa da Basiru Garba, Ladan Muhammad, Hassan Ali, Abubakar Sa’adu, Ahmad Muhammad, Aminu Hamisu, Muhammad Abdullahi, Suleiman Abdullahi, Abubakar Auwalu, Faruk Abdullahi, Isah Ismail, Hassan Aliyu, da Usman Muhammad – dukkaninsu daga sassa daban-daban na Jigawa da Nguru, Jihar Yobe.
A yayin samamen, jami’an ƴan sandan sun ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri ciki har da Exol (ƙwaya 704), Tramadol (264), Diazepam (3), D5 (2,042), roba mai wari (48), tabar wiwi (4 blocks da 148 wraps), wayar Vivo (da ake zargin ta sata ce), farare da jajayen kafso (602), da wasu ruwayen maye har lita 6.
Sanarwar ta ce an miƙa waɗanda ake zargi zuwa kotu bayan kammala cikakken bincike.
Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya gargaɗi duk masu aikata miyagun laifuka da su daina ko kuma su fuskanci hukuncin doka, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci domin taimakawa rundunar wajen dakile aikata laifi.
Sanarwar ta ƙare da tabbatarwa jama’a cewa rundunar ƴan sanda na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a dukkan ƙananan hukumomin jihar.