Sanata Natasha za ta koma majalissa bayan shafe watanni shida a dakace
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, za ta koma Majalisar Dattawa a ƙarshen watan nan bayan kammala dakatawar da aka yi mata ta tsawon watanni shida, in ji lauyanta, Victor Giwa.
Giwa ya shaida wa manema labarai cewa sanatar, yanzu haka tana hutawa a London, amma ta riga ta shirya komawa zaman majalisa ranar 23 ga Satumba lokacin da majalisar za ta sake komawa aiki bayan hutun da ta yi.
A ranar 6 ga Maris ne aka dakatar da sanatar bisa zargin rashin biyayya bayan ta ƙi karɓar sauyin kujerar da aka yi mata a zauren majalisa, lamarin da ta danganta da ƙorafinta na cin zarafin neman yin lalata da ita, wanda ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, zargin da majalisar ta yi watsi da shi.
Lauyanta ya tabbatar da cewa babu wata matsala a yanzu, yana mai cewa, “Mun samu tabbaci cewa shugabannin majalisar za su tarbe ta. Babu wani shinge a yanzu, duk sauran shari’o’in ma za su zama tarihi kawai.”