Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta saki zazzafan gargaɗi kan barazanar DSS na hana amfani da manhajar X a Najeriya
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta umartar Hukumar Tsaron Ƙasa (DSS) ta janye barazanar hana X (Twitter a da) a Najeriya, suna masu cewa hakan zai zama take haƙƙin ƴancin faɗar albarkacin baki da samun bayanai.
A wata sanarwa da wakilinmu ya samu, ƙungiyar ta tunatar da hukuncin Kotun ECOWAS wadda ya bayyana samun damar amfani da Twitter a matsayin haƙƙin ɗan adam na asali, da kuma batun da ya faru a mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da aka dakatar da Twitter, inda kotu ta ayyana hakan a matsayin na ba bisa ƙa’ida ba.
Sanarwar ta ce: “Kowace takura kan haƙƙin faɗar albarkacin baki dole ne ta cika ƙa’idojin doka, buƙata, da daidaito, bisa yarjejeniyar ƙasa da ƙasa. DSS ba za ta iya matsa lamba kan X don tsare bayanan yanar gizo ko rufe kafofin sada zumunta ba, saboda hakan karya haƙƙin ƴancin faɗar albarkacin baki ne.”
Ƙungiyar ta yi barazanar ɗaukar mataki a kotu idan DSS ba ta janye wannan barazana nan take ba, tana mai gargaɗin cewa hakan zai sake kawo illa ga demokaraɗiyya da martabar Najeriya a idon duniya.