Za a sami rashin lafiyar wata mai tsanani “blood moon” a yau Lahadi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka

37

Mutanen Najeriya da wasu ƙasashen Yammacin Afirka na shirin shaida wani gagarumin al’amari na sararin samaniya a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, yayin da za a samu cikakken kusufin tun daga ƙarfe 8:00 na dare agogon Yammacin Afirka.

Rahoton Hukumar Talabijin ta Ƙasa (NTA) ya bayyana cewa kusufin zai ɗauki kusan mintuna 83, yana mai canza launin wata zuwa ja mai ɗaukar hankali duk mazauna faɗin yankin.

An tabbatar da cewa ƙasashen da za su fuskanci wannan abin mamaki sun haɗa da Najeriya, Ghana, Kamaru, Gabon, Equatorial Guinea, Benin, Togo, Nijar, Chadi da Sao Tome da Principe, in ji NTA a rahotonta na Lahadi da wakiliyarmu Maryam Ayuba ta bibiya.

“Wasu ƙasashen na iya rasa farkon matakan kusufin saboda watan zai fito kusa ko yayin samun cikakken kusufin, amma cikakken abin mamakin zai bayyana a yawancin sassan Najeriya,” in ji rahoton.

Masana sun bayyana cewa kusufin wata na faruwa ne idan Rana, Duniya da Wata suka bi layi ɗaya, sai duniya ta sa inuwarta a kan fuskokin wata.

NASA ta tabbatar a shafinta cewa kusufin wata na iya kasancewa cikakke, na wani ɓangare, ko na gefe, inda na wannan Lahadin zai bayyana ma a Turai, Afirka, Asiya da Ostiraliya.

Ba kamar kusufin rana ba, wannan kusufi na wata ba shi da haɗari ga masu kallonsa da ido kai tsaye.

Rahotanni sun nuna cewa wasu yankunan da ke da ƙarancin hasken wutar lantarki kamar Yobe da Borno na iya zama wurin da za a fi samun kallo mafi kyau a Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.