Ƴan Sanda a Bangladesh sun fara kame bayan wasu masu iƙirarin aƙida sun yi ta’addanci wa kabari da ƙone gawar shehin Sufaye

Ƴan sanda a Bangladesh sun fara neman waɗanda suka aikata laifi bayan ɗaruruwan masu tsattsauran ra’ayin addini sun lalata kabarin wani malami mai cike da cece-kuce, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu kusan 50.
Wakilinmu Hussaini Isah ya tattaro daga kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, harin ya faru ne ranar Juma’a a Rajbari, inda mambobin ƙungiyar Iman-Aqida Raksha Committee suka yi wa maƙabartar Nurul Haque Molla, wanda aka fi sani da “Nura Pagla”, dirar mikiya.
Shaidu sun ce an tono gawar Molla daga kabarinsa aka kuma ƙone ta saboda ginin kabarin ya yi kama da Ka’aba, sannan shi kuma ya taɓa iƙirarin cewa shi ne Imam Mahdi, wanda hakan ya jawo masa suka daga ɓangaren ƴan Sunni masu tsattsauran ra’ayi.
Kwamandan ƴan sanda na Rajbari, Md Kamrul Islam, ya ce, “Mun fara gano waɗanda suka aikata laifin, ba wanda zai kuɓuta.”
Wani mai gadi, Russell Molla ya rasu a harin, yayin da uku daga cikin waɗanda suka ji rauni ke cikin mawuyacin hali.
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Muhammad Yunus, mai lambar yabo ta Nobel, ta yi Allah-wadai da harin, tana kiransa da “abun ƙyama” tare da alƙawarin kare mutuncin rayuwa da kuma bin doka.
Mai kare haƙƙin bil’adama, Abu Ahmed Faijul Kabir, ya bayyana lamarin a matsayin wani ɓangare na “yawaitar rashin jurewa addini da al’adun wasu”, yana gargaɗin cewa, matsin lamba kan al’adun Sufaye da shirye-shiryen al’adu a ƙasar zai zamewa Bangladesh babban ƙalubale.