Tambuwal ya ce, ya “ƙuduri aniyar kawar da gwamnatin Tinubu daga mulkin Najeriya a 2027”

20

Times Hausa ta gano cewa, tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da wasu mutane a Najeriya na wani shiri da nufin ganin gwamnati mai ci ta sauƙa daga mulki a shekarar 2027 ta hanyar demokaraɗiyya.

Tambuwal, wanda ya ke cikin manyan jiga-jigan adawa a sabuwar haɗakar jam’iyyun siyasar Najeriya, a tattaunawarsa da Channels a jiya Juma’a ya ce, “Ina cikin wani tsari – bisa doka da biyayya ga demokaraɗiyya – wanda, da yardar Allah, zai kawo ƙarshen shugabancin wannan gwamnati.”

Ya ƙara da cewa, “Da taimakon Allah da goyon bayan ƴan Najeriya, za mu kawar da waɗannan mutane daga gwamnati,” yana mai ƙaryata jita-jitar cewa shirin yana da wata manufa ta ƴan Arewa kaɗai.

“Wannan yarjejeniya ce ta ƙasa baki ɗaya. Peter Obi ɗan Arewa ne? Aregbesola daga Osun yake,” in ji shi, yana mai jaddada cewa canjin shugabanci ya kamata ya faru ta hanyar doka da demokaraɗiyya a ranar 29 ga Mayu, 2027.

Tambuwal ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza cika alƙawarin demokaraɗiyya ga ƴan ƙasa, yana mai cewa iƙirarin cewa shugaban ƙasa ba zai iya faɗuwa a zaɓe ba “wasa ne kawai”.

“Ba doka ba ce cewa dole sai ya ci a 2027. Duk ƙoƙarin da ake yi na nuna kamar Bola Tinubu ba zai iya faɗuwa ba – shirme ne,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Za a iya kayar da shi. Na yi imani da hakan, kuma ina aiki tare da shugabannin haɗaka domin ganin hakan ya tabbata a ƙasa. Ba wai game da Bola Tinubu bane, amma yanayin yadda yake tafiyar da ƙasar shine.”

A ƴan watannin da suka wuce, wasu fitattun ƴan siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Peter Obi, tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da tsohon gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi, suka kafa haɗakar da ake ganin na da ƙarfin iya kawar da jam’iyya mai ci.

Sun yi alƙawarin sauya gwamnati a 2027, duk da cewa jam’iyyar APC ta yi watsi da wannan barazanar tana mai yi musu dariya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.