An Bayyana Sake Ɓarkewar Cutar Ebola, WHO ta Koka Kan Yiwuwar Samun Yaɗuwa

Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun tabbatar da ɓarkewar cutar Ebola a lardin Kasai, inda aka samu mutane 28 da ake zargin sun kamu, da kuma mace-macen wasu 15 ciki har da ma’aikatan lafiya huɗu.
Wani jawabi daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Alhamis ya nuna cewa ɓarkewar cutar ta faru ne a yankunan Bulape da Mweka, inda aka gano mutanen da ke fama da zazzaɓi, amai, gudawa da zubar da jini.
Ɓarkewar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu cututtuka da rikice-rikicen jin ƙai ke damun yankin Afirka ta Tsakiya da ta Yamma. Ɓarkewar da ta gabata a Equateur a watan Afrilun 2022 an shawo kanta cikin watanni uku daga baya.
Kasai ta samu ɓarkewar Ebola a shekarar 2007 da 2008.
An tabbatar da cewa nau’in Zaire ne na cutar a ranar 3 ga watan Satumba.
WHO ta ce tawagar kai ɗaukin gaggawa ta haɗa kai da ƙwararrunta don ƙarfafa sa ido, bayar da magani da kariya don hana yaɗuwar cutar a lardin.
Hakanan, an tura tan biyu na kayayyaki daban-daban, ciki har da kayan kariya da na’urar bincike zuwa yankin da ke da wahalar shiga.
“Muna aiki cikin gaggawa don dakatar da yaɗuwar ƙwayar cutar da kare al’umma,” in ji Dr. Mohamed Janabi, Daraktan WHO a Afirka.
“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin lafiya don ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen ɓarkewar cikin gaggawa.”
WHO ta yin gargaɗin cewa adadin masu kamuwa na iya ƙaruwa, yayin da ake ƙoƙarin gano duk wanda ya yi hulɗa da masu cutar domin a yi musu rigakafi, ciki har da tura allurar rigakafin Ebola Ervebo guda 2,000 daga Kinshasa zuwa Kasai.