Ƴan Sandan Jigawa sun wayar da kan ƴan jari-bola kan kare kai daga taka bom yayin tsince-tsince

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta gudanar da taron wayar da kai ga ƴan kasuwar shara da ƙarafa (ƴan jari-bola) a jihar domin faɗakar da su kan haɗarin abubuwa masu fashewa (irin su bom).

Wakilinmu ya tattaro cewa, taron wanda aka gudanar a ranar Laraba 8 ga Oktoba, 2025, ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴan Sanda, CP Dahiru Muhammad, tare da taken “Explosive Ordinance Risk Awareness and Sensitization Campaign.”

Kwamandan Sashen EOD-CBRN Base 24, Dutse, SP Abdurrahman Abubakar Malami, ya gabatar da lacca mai zurfi kan yadda ake gane abubuwan fashewa da yadda ake kare kai daga gare su.

Ya kuma nuna muhimancin kai rahoto cikin gaggawa ga ofishin ƴan sanda idan an ga wani abu da ake zargi.

Taron ya samu halartar mai ba Gwamnan Jihar Jigawa shawara kan harkokin tsaro, Dr. Usman Muhammad Jahun, da wakilin Sarkin Dutse, Alhaji Umar Barwan Dutse, da shugabannin ƙungiyar ƴan jari-bola daga ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Mai magana da yawun ƴan sanda, SP Shiisu Lawan Adam, ya ce wannan shiri na nuna ƙudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyi ta hanyar haɗin kai da jama’a.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.