Ƴan sanda sun cafke sojan ƙarya da wasu ɓarayin motoci a Jigawa

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wani sojan bogi da wasu mutane uku da ake zargi da satar motoci a ƙaramar hukumar Kafin Hausa.

Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar cewa lamarin ya faru ne ranar 8 ga Satumba, 2025, lokacin da waɗanda ake zargin suka yi hatsari da wata motar Golf mai launin shuɗi da suka sace a garin Agura, kafin su tsere daga wurin.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Kabiru Musa mai shekara 35 daga Rimin Kebe a Kano; Umar Ali mai shekara 25 daga Haye Quarters a Kano; da Sabiu Bashir mai shekara 25 daga ƙauyen Tokarawa, Jihar Kano.

Bincike ya nuna cewa Kabiru Musa, wanda ya bayyana kansa a matsayin Lance Corporal na rundunar Guards Brigade a Abuja, ba soja ba ne, illa mai satar matsayi, inda aka gano katunan ATM guda bakwai, lasisin tuƙi guda biyu, da sauran abubuwan da ake zargin ana amfani da su wajen aikata damfara a hannunsa.

An gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike a sashen SCID Dutse.

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’an Kafin Hausa bisa jajircewarsu da nuna ƙwarewa, tare da nanata aniyar rundunar wajen kawar da miyagu da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kuma yi kira ga al’umma su ci gaba da ba da bayanai masu inganci da wuri domin taimaka wa jami’an tsaro wajen hana aikata laifuka.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.