Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar da cafke mutane 21 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ɓarayin dabbobi da masu fasa-gidaje a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarar tare da ƙwato dabbobi da kayayyakin da ake kyautata zaton na sata ne.
Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar da kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ya fitar, cewa a ranar 27 ga Satumba, 2025, jami’an tsaro na Dutse sun cafke wani Gaddafi Ya’u mai shekaru 25 a unguwar Kwanar Balbelu bisa zargin fasa-gidaje.
An ƙwato na’urar stabilizer guda ɗaya, huluna 9, wuka guda ɗaya, screwdriver, da allunan Diazepam guda 9 daga hannunsa.
Rahoton ya tabbatar cewa an kammala bincike kuma an gurfanar da shi gaban kotu.
Bugu da ƙari, jami’an sintiri a Jahun, Birniwa, Garki da Aujara sun ƙwato shanu biyu da tumaki 12 da ake zargin an sace su, tare da kama mutum biyu da ake ci gaba da bincike a kansu.
Haka kuma, jami’an tsaro sun cafke mutane huɗu a Jahun, Yalwawa da Kachi bisa zargin satar wayoyin lantarki da injin janareta da compressors guda biyu na na’urar sanyaya iska.
A wani samame da a kai a Dutse, Ringim, Gwiwa, Takur, Sara da Basirka, an cafke mutane 21 da ake zargin masu safarar miyagun ƙwayoyi ne.
An gano kwayoyi iri daban-daban ciki har da Tramadol guda 420, Exol guda 330, tabar wiwi da aka nannaɗe guda 240, D5 guda 231, da sauran magunguna da kayan maye, tare da kuɗaɗen da ake zargin kuɗin da aka samu ta haramtaccen kasuwanci ne har naira dubu arba’in da ɗari bakwai.
Kwamishinan Ƴan Sandan ya yabawa jajircewar DPOs na Jigawa da jami’an da suka gudanar da ayyukan, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen murƙushe masu aikata laifi a jihar.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook