Ƴan sanda sun ƙara kama masu aikata laifuka daban-daban a Jigawa, sun ƙwato wayoyi, motoci da miyagun ƙwayoyi
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Rundunar Ƴan Sanda ta Jigawa ta bayyana nasarorin da ta samu wajen kama masu aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar, ƙarƙashin jagorancin CP Dahiru Muhammad.
Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar rundunar cewa, a Ofishin Ƴan Sanda na Yalleman, an kama Umar Adamu, ɗan shekaru 18, bisa zargin satar wayoyi da SIM cards.
A Birnin Kudu, an ƙwato wani babur da ake zargin na sata ne daga hannun Basiru Isma’il, ɗan shekara 28.
A ofishin Shuwarin, an kama masu satar na’urorin lantarki, yayin da a ofishin Dutse, an kama sanannen mai sayar da miyagun ƙwayoyi, Jamilu Ibrahim (wanda ake kira Xina), inda aka ƙwato miyagun ƙwayoyi da kuɗi naira 163,500.
A ofishin Yalwawa na Dutse, an kama Abdullahi Alhassan, Umar Musa da Sagiru Umar, da kayan da suka sata ciki har da TV Samsung, na’ura mai ƙwaƙwalwa da iPhone.
SP Shiisu Lawan Adam, jami’in hulɗa da jama’a, ya yaba wa jajircewar jami’an, sannan ya roƙi jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai don daƙile aikata laifuka.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook