Ƴan Sanda a Jigawa sun damƙe ƴan ƙwaya, ɓarayin shanu da masu lalata kayan gwamnati, sun bayyana sunayensu

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’anta sun cafke wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, satar shanu da tumaki, da kuma lalata wayoyin wutar lantarki a wasu yankuna na jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar ranar Alhamis, 18 ga Satumba 2025, a Dutse.

Kama masu lalata wayoyin lantarki

Wakilinmu ya tattaro cewa a ranar 16 ga Satumba 2025, da misalin ƙarfe 8:00 na safe, tawagar sintiri ta Gwaram Division ta cafke Abdul Umar (mai shekaru 19) da Sahaba Sani (mai shekaru 19), dukkansu mazauna Unguwa Uku ta Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano.

An kama su ne da wayoyin lantarki da aka lalata daga fitilun kan titi a garin Tsohuwar Gwaram, inda suka amsa laifinsu bayan bincike.

Satar shanu daga ƙasar Nijar

Haka kuma, a ranar 16 ga Satumba 2025 da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, jami’an Birniwa Division sun cafke Shafiu Kwalle (mai shekaru 22), ɗan asalin Machina a Jihar Yobe, da kuma Abubakar Sadiq (mai shekaru 23), ɗan Rugar Aremari, Jamhuriyar Nijar, ɗauke da shanu biyu da ake zargin na sata ne.

Bincike ya tabbatar da cewa sun sato dabbobin ne daga ƙauyen Kapirka a Jamhuriyar Nijar, kuma ɗaya daga cikin shanun ya kasance mallakin Alhaji Umar Garanda mai shekaru 50, daga Machina.

Kama ƴan ƙwaya

Kakakin rundunar ya ce daga 13 zuwa 17 ga Satumba 2025, jami’an Fanisau, Birniwa, Gujungu, Yalwawa, da Yankwashi duk a Jigawa sun kai samame a maɓoyar miyagun ƙwayoyi.

An cafke mutane 14, tare da ƙwato tabar wiwi, magungunan sa maye, da wasu abubuwa da ake amfani da su wajen yin maye, ciki har da Tramadol, Diazepam, Exol, da kuma wasu robobi masu warin maye.

Satar shanu a Sara

Bugu da ƙari, a ranar 13 ga Satumba 2025 da misalin ƙarfe 5:30 na safe, wani mai suna Inusa Isiyaku daga Ruwan Kawoni, Sara, ya kai ƙara cewa an sace masa shanu biyu da ƙimar su ta kai naira miliyan 2.

Ƴan sanda sun gano shanun a motar Ford mai lambar BWR 203 CE, inda aka cafke direban motar, Aminu Isah (mai shekaru 37) daga Zaria, yayin da wasu suka tsere.

Bincike a Ringim

A ranar 10 ga Satumba 2025, jami’an Ringim tare da Safer Highway da vigilante na Jigawa sun cafke Hassan Musa (mai shekaru 25), Adamu Abdullahi (mai shekaru 45), da Shuaibu Dahiru (mai shekaru 47), ɗauke da saniya a cikin mota ƙirar Golf 3.

Bincike ya kai ga gano ƙarin saniya da tumaki 11 a gidan Shuaibu, kafin a tura batun zuwa SCID Dutse.

SP Shiisu ya tabbatar da cewa duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.