Ƴan Najeriya sama da miliyan 20 ba sa samun damar amfani da intanet, ana shirin samar da kilomita 90,000 na netwok
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijani, ya bayyana cewa mutane fiye da miliyan 20 a Najeriya har yanzu ba su da damar shiga intanet.
TIMES HAUSA ta tattaro daga zaman sauraron jama’a a Majalisar Dokoki kan ƙudurin da ke neman tilasta dukkan ma’aikatu su koma tsarin aiki na dijital cewa, ministan ya bayyana gagarumin aikin faɗaɗa hanyar sadarwa a ƙasar.
Ya ce, “Yanzu haka muna aiki tare da Majalisar Dokoki domin shimfiɗa kilomita 90,000 na firam-optic da za su haɗa yankuna shida, jihohi da ƙananan hukumomi.”
Ya ƙara da cewa an ƙaddamar da aikin gina hasumiyoyi 4,000 domin samar da sadarwa a yankunan da ba su da isasshen intanet a Najeriya.
Bambancin shiga intanet a Najeriya
Najeriya, duk da kasancewarta babba a tattalin arziƙi a Afirka. na fama da gagarumin rata tsakanin birane da karkara.
Yankuna kamar Lagos, Abuja da Port Harcourt na samun cigaba, amma jihohi irin su Kebbi, Taraba, Niger, Cross River da wasu yankunan Kudu-maso-Kudu har yanzu na cikin duhun intanet.
TIMES HAUSA ta tattaro cewa matsalolin sun haɗa da rashin wutar lantarki, tsadar data ta intanet, kariyar tsaro a yankunan karkara, da jinkirin shimfiɗa layukan sadarwa da hasumiyoyi.
Ministan ya ce tattalin arziƙin dijital ya tashi daga 16% zuwa 19% a cikin GDP, kuma gwamnati na shirin kai ƙasar ga tattalin arziƙin dala tiriliyan 1 kafin 2027, tare da samun 21% daga dijital.
Amfanin dokar dijital
Ya ce ƙudurin dokar da ake tattaunawa zai ba da izinin amfani da takardun lantarki da sa hannun dijital tare da ƙarfafa tsaron yanar gizo da amfani da Fasahar Ƙirƙiren Hankali (AI) wajen gudanar da gwamnati.
“Wannan doka za ta shimfiɗa tubalin tattalin arziƙin nan gaba. Ba wai don shugaban ƙasa ko minista ba ne, don makomar Najeriya ne gaba ɗaya.”
Martanin Majalisar Dokoki
Shugaban Kwamitin ICT na Majalisar Dattawa, Shuaib Salisu, ya ce dokar za ta zama ginshiƙin da zai jagoranci mu’amalar lantarki a Najeriya.
Shugaban Kwamitin ICT na Majalisar Wakilai, Adedeji Olajide, ya ce dokar za ta sauya tsarin yin aiki a gwamnati, da ƙara tabbatar da gaskiya da inganci.
NCC, NIGCOMSAT, NIPOST, Galaxy Backbone da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati duk sun amince da ƙudurin.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook