Ƙungiyar Matasan Najeriya ta yaba wa Tinubu kan zuba jari a matasa, ta amince da Shettima a matsayin ɗan takara
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ƙungiyar Matasan Najeriya (NYCN), Yankin Arewa maso Gabas, ta bayyana godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa saka hannun jari da yake yi a matasa, tare da jaddada aniyar haɗin kai domin kawo ci gaba.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar 12 ga Satumba 2025 bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Damaturu, Jihar Yobe, ƙarƙashin jagorancin Comrade Yusuf Ibn Tom, an buƙaci dukkan mambobin ƙungiyar su haɗa kai domin gudanar da taron gangamin ƙasa cikin gaskiya da aminci.
Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar bayan taron cewa, yankin ya yaba da shirye-shiryen matasa da Ministan Harkokin Matasa, Comrade Olawande Emmanuel Ayodele, ke aiwatarwa.
Yankin ya kuma jaddada goyon bayansa ga zaman Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar 7 ga Agusta 2025.
Haka zalika, yankin ya yaba da hukuncin yankin kudu na ƙungiyar NYCN bisa amincewa cewa shugabancin ƙasa na ƙungiyar ya koma yankin arewa a babban taron da ke tafe.
Sanarwar ta bayyana cewa, an ɗauki tsarin mulkin NYCN na 2012 a matsayin doka mai jagorantar taron, tare da amincewa da tsarin wa’adin mulki na shekara huɗu ga dukkan shugabanni na ƙasa.
An bayyana Comrade Shettima Umar a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa na NYCN da yankin Arewa maso Gabas ya yarda da shi, tare da Cosmos Danladi a matsayin ɗan takara a muƙamin Mataimakin Sakataren Hedikwatar ƙungiyar, da Gambo Abubakar a muƙamin Jami’in Shirye-shirye.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa za ta shiga taron zaɓen ƙasa da ke zuwa ranar 7 ga Oktoba 2025 a Abuja cikin shiri da ɗorewar haɗin kai.
Ƙungiyar ta yaba wa gwamnonin Arewa maso Gabas da kuma Kwamishinonin Harkokin Matasa na yankin bisa tallafi da jajircewarsu wajen raya matasa da gina shugabanci nagari.
“NYCN Arewa maso Gabas ta ƙuduri aniyar yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da taron gangamin ƙasa mai nasara da haɗin kai. Haka kuma muna godiya ga shugabannin matasa da ƙungiyoyi a yankin bisa jajircewa wajen kare muradun matasan Najeriya,” in ji sanarwar.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook