Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Wata tawaga daga ƙungiyar Colleges of Education Academic Staff Union (COEASU) ta kai ziyarar ta’aziyya ga majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel, bisa rasuwar dalibi mafi ƙwarewa a fannin Mathematics/Physics na NCE 2, Khalid Yunusa, wanda ya rasu a hanyar zuwa Gusau domin rubuta jarrabawar neman tallafin karatu na ƙungiyar.
Wakilinmu ya rawaito cewa, tawagar ƙarƙashin jagorancin shugaban COEASU na ƙasa, Comrade Dr. Smart Olugbeko, ta bayyana alhinin ƙungiyar kan wannan babban rashi, inda ya ce ƙungiyar ta girgiza da mutuwar matashin.
Ya kuma sanar da cewa za a mayar da sunan tallafin karatu na ƙungiyar sunan marigayin domin girmama shi har abada.
Muƙaddashin shugaban majalisar gudanarwa na kwalejin, Dr. Yahaya Idris, ya nuna godiya da wannan karamci na ƙungiyar, tare da tabbatar da cewa makarantar ma za ta saka sunan ɗalibin a ɗaya daga cikin gine-ginen ta.
A cewarsa, “Wannan mataki zai tabbatar da cewa sunan Khalid Yunusa ba zai taɓa gogewa ba a tarihin makarantar.”
Tun kafin wannan ziyara, shugaban ƙungiyar na shiyyar arewa maso yamma, Comrade Abdullahi Mati Gada, tare da wasu jami’ai daga kwalejin, sun ziyarci kwalejin da iyalan marigayin a garin Idanduna, Karamar Hukumar Miga, Jihar Jigawa, domin jajantawa da bayyana alhini.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook