Fubara ya yi jawabi ga al’ummar Rivers karo na farko bayan ƙarewar dokar ta-ɓaci a jihar, ya gode wa…
Wakilinmu ya tattaro cewa Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi jawabi ga jama’ar jiharsa a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025, bayan ƙarshen wa’adin watanni shida na dokar ta-ɓaci da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya tun a!-->…
EFCC ta ritsa ƴan damfara da intanet har su 19, ta kama su tare da ƙwace kayan aikinsu
Wakilinmu ya tattaro daga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, cewa jami’anta daga ofishin Kaduna sun kama mutane 19 da ake zargi da yin damfara ta intanet a ƙaramar hukumar Lapai ta Jihar Neja.
An ce an kama su ne a ranar!-->!-->!-->…
Annobar amai da gudawa ta kashe mutane 58, ta kwantar da wasu da dama a Bauchi
Aƙalla mutane 58 sun rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar sabuwar annobar cutar amai da gudawa da ta ɓulla a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 na Jihar Bauchi.
Bayanan da Daily Trust ta tattara daga ofishin gwamnatin jihar sun ce akwai!-->!-->!-->…
Atiku ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai uku da suka lashe gasar Turanci a Ingila
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jagoran adawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ɗauki nauyin karatun ƴan mata uku da suka lashe gasar TeenEagle Global Finals ta Turancin Ingilishi da aka gudanar a Ingila.
BBC Hausa ta tattaro a wata!-->!-->!-->…
Matasan ƴan kasuwa a Jigawa sun lashe gasar samun tallafin naira miliyan biyu don bunƙasa kasuwanci
Aƙalla matasa takwas daga cikin sabbin ƴan kasuwa 80 a Jigawa waɗanda Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) ta horas sun samu tallafin naira miliyan biyu don inganta kasuwancinsu.
Ingantattun bayanai da PUNCH ta!-->!-->!-->…
Gwamna Namadi ya bayyana matsayar Jigawa kan shan giya, “Doka ce kan kowa, ba ta bar kowa ba”
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada matsayin gwamnatin jihar kan shan giya, yana mai bayyana cewa dokar ba wai an tsara ta ba ne domin tauye haƙƙin wani, illa dai domin daidaita lamuran da suka saɓa wa doka, al’ada da!-->…
Ƙaramar Hukumar Hadejia a Jigawa ta fara gina ramin zuƙe ruwa mai tsawon kilomita uku don magance…
Ƙaramar Hukumar Hadejia a jihar Jigawa ta fara aikin gina rami mai tsawon kilomita uku domin bai wa ruwa hanya daga wani tafki zuwa Kogin Hadejia, a wani yunƙuri na magance matsalar ambaliya da ke addabar al’ummar yankin.
Wannan na!-->!-->!-->…
Za a samu ruwan sama a kusan dukkan jihohin Najeriya a yau Juma’a – NiMet
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da cewa za a samu ruwan sama mai haɗuwa da guguwar iska a sassa daban-daban na ƙasar nan ranar Juma’a, 19 ga Satumba 2025.
Wakiliyarmu ta tattaro daga rahoton NiMet cewa za a samu!-->!-->!-->…
Hukumar Hana Cin Hanci ta Jigawa ta ƙwato sama da naira miliyan 200, ta warware ƙorafe-ƙorafe
Hukumar Karɓar Korafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (PCACC) ta bayyana cewa ta ƙwato sama da naira miliyan 200 daga cikin korafe-korafen da jama’a suka shigar, tun bayan da aka kafa ta a farkon shekarar 2024.
Wakilinmu!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda a Jigawa sun damƙe ƴan ƙwaya, ɓarayin shanu da masu lalata kayan gwamnati, sun bayyana…
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’anta sun cafke wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, satar shanu da tumaki, da kuma lalata wayoyin wutar lantarki a wasu yankuna na jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin!-->!-->!-->…