Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da cewa za a samu ruwan sama mai haɗuwa da guguwar iska a sassa daban-daban na ƙasar nan ranar Juma’a, 19 ga Satumba 2025.
Wakiliyarmu ta tattaro daga rahoton NiMet cewa za a samu ruwan sama da guguwar iska a wasu sassan Taraba da safe, yayin da da yamma ake sa ran samun hadari mai ɗauke da iska da ruwan sama a Adamawa, Bauchi, Kaduna, Taraba, Gombe, Kano, Jigawa, Borno da Yobe.
Hasashen ya nuna cewa za a fara da yanayi mai ɗan sanyi tare da hasken rana, sai dai daga baya ana sa ran ruwan sama mai yawa a yawancin sassan yankin.
A yankin Kudu kuma, NiMet ta bayyana cewa za a samu ruwan sama marar yawa da safe a Cross River da Akwa Ibom, sannan daga baya ana sa ran samun hadiri mai ɗauke da iska da ruwan sama a mafi yawan sassan kudu.
NiMet ta ja hankalin jama’a cewa ruwan sama zai iya kawo tsaiko a harkokin waje, kuma direbobi su yi taka-tsantsan saboda matsalar rashin gani sosai dalilin duhun hanya.
Haka kuma ta shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar ambaliyar ruwa da su ɗauki matakan kariya.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook