Za a sami ruwan sama da hadiri mai iska a sassa da dama na Najeriya a yau Laraba – NiMet

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayin yau Laraba, 17 ga Satumba, 2025.

Wakiliyarmu ta tattaro cewa a Arewa, za a samu ruwan sama da hadiri mai iska a wasu sassan Kaduna, Kebbi, Sokoto, Adamawa da Taraba da safe, yayin da da yamma kuma za a samu a sassan Yobe ta Kudu, Borno ta Kudu, Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi, Gombe da Kebbi.

A tsakiyar ƙasar, yanayin zai kasance cikin gajimare da ruwan sama marar yawa a wasu wurare, yayin da yankin Kudancin ƙasar zai fuskanci ruwan sama mai ɗaukewa lokaci-lokaci da guguwar iska a jihohin Oyo, Ogun, Edo, Rivers, Delta, Cross River da wasu sassa.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa ruwan sama zai iya jawo tangarɗa ga harkokin waje da haɗarin hanya.

Haka kuma ta ja hankalin mazauna yankunan da ke da tarihin ambaliya da su ɗauki matakan kariya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

NiMET
Comments (0)
Add Comment