Wata sabuwar cuta ta yi ajalin yara a Borno, iyayensu kuma na kwance a asibiti

An shiga jimami a ƙauyen Kukurpu da ke yankin Kwajaffa a Ƙaramar Hukumar Hawul, Jihar Borno, bayan da wasu yara huɗu ƴan gida ɗaya suka rasu a dalilin wata mummunar cuta, yayin da iyayensu ke samun kulawa a asibiti.

Zagazola Makama, mai bincike kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya rawaito cewa lamarin ya auku ne da safiyar Alhamis, bayan da maƙwabtan gidan da lamari ya faru suka fara damuwa sakamakon kiraye-kirayen waya da suka yi ta yi wa mai gidan, Muktari Idrisa, mai shekara 35, ba tare da amsa ba.

Wani maƙwabcin Mukhtari, Bukar Musa, daga bisani ya samu damar yin magana da matar Idrisa, Maimuna, wadda ta bayyana cewa dukkan su a gidan sun kamu da rashin lafiya mai tsanani, ba sa iya ko motsawa.

Daga nan ne, maƙwabtan suka yi maza-maza suka shiga gidan, inda suka tarar da Idrisa, matarsa, da yaransu huɗu a kwance magashiyan.

Yaran da suka rasu sun haɗa da Idrisa Muktari, Hauwa Muktari (9), Binta Muktari (6), da Saidu Muktari (1).

Jami’an tsaro da ƙwararrun likitoci sun garzaya wajen, amma bayan zuwa asibiti an tabbatar da mutuwar yara huɗun, yayin da aka kwantar da iyayen ana kula da su.

An kai gawarwakin yaran ɗakin ajiye gawa na asibitin, kafin daga bisani a miƙa su ga dangi domin yin jana’iza bisa ƙa’idar Musulunci.

Hukumomi sun bayyana cewa ba a gano musabbabin lamarin ba har yanzu, amma ƴan sanda sun tabbatar da cewa sashen binciken manyan laifuka (CID) da ke Maiduguri ya fara yin cikakken bincike a kai.

Wannan mummunan yanayi mai ɗauke da tashin hankali dai, ya jefa ƙauyen manoma na Kukurpu na Jihar Borno cikin fargaba da zub da hawaye, inda maƙwabtan ke ƙoƙarin jure rashin da suka fuskanta daga iyalin gida ɗaya kacal.

Bornorashin lafiya
Comments (0)
Add Comment