Manyan masana da shugabannin fannoni daban-daban na Najeriya, ciki har da Farfesa Pat Utomi, tsohon Shugaban INEC Farfesa Attahiru Jega da tsohuwar Ministar Ilimi, Dr. Oby Ezekwesili, za su ƙaddamar da sabuwar tafiya domin neman gyaran demakaraɗiyya mai suna Alliance for Defence of Democracy (ADD) a ranar 1 ga Oktoba.
Wakilinmu, Faruk Ahmad ya samo daga kakakin National Consultative Front (NCFront), Hamisu San Turaki, cewa wannan mataki wani gagarumin yunƙuri ne na samar da sauyin tafiyar siyasa da zai taimaka wajen ɗora tsarin zaɓe na ƙasa kan turbar gaskiya kafin babban zaɓen 2027.
Cikin ƴan tafiyar akwai kuma shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero; manyan lauyoyi Dr. Olisa Agbakoba da Femi Falana; tsohon mai ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed; Farfesa Kingsley Moghalu; da fitaccen ɗan NNPP, Buba Galadima.
An bayyana cewa dandalin ADD zai mayar da hankali kan ƙirƙirar dokokin zaɓe masu inganci, ciki har da tilasta amfani da na’urar lantarki wajen aika sakamakon zaɓe, hukunta masu siyan ƙuri’u, da samar da damar kaɗa kuri’a da wuri ga mazauna ƙasashen waje.
Wakilin namu ya kuma gano cewa an shirya babban taron ƙasa na ƙaddamar da tafiyar a ranar 1 ga Oktoba, ranar zagayowar samun ƴancin Najeriya inda aka gayyaci manyan ƴan ƙasa, ƙungiyoyin ƙwadago da na farar hula don ƙarfafa muradun wannan sabuwar tafiya ta gyaran tsarin demokaraɗiyya a Nijeriya.